fbpx
Saturday, December 4
Shadow

‘Yan bindiga sun kashe mutum 6 a Katsina

Yan bindiga sun kashe akalla mutum shida tare da garkuwa da wasu da dama a kauyen Unguwar Samanja na jihar Katsina ranar Lahadi.

Kamar yadda jaridar Premium Times ta ambato wani mazauna kauyen Daudawa mai makwabtaka yana cewa, maharan sun isa kauyen kusan karfe shida na yamma, a lokacin da jama’a ke shirin sallar magariba.

Unguwar Samanja na karkashin karamar hukumar Faskari, wadda ta dade tana fuskantar hare-hare daga yan bindiga.

Kazalika tana daga cikin kananan hukumomi 13 da aka katse sadarwa, a wani bangare na yaki da yan bindiga.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *