fbpx
Saturday, October 16
Shadow

Yan bindiga sun kashe mutum biyu, sun sace malami a Kaduna

Yan bindiga sun sace wani malamin Larabci da Addinin Musulunci a yankin Kuregu a Karamar Hukumar Zariya ta Jihar Kaduna.

Daily Trust ta ruwaito cewa an kuma kashe mutane biyu a yayin lamarin wanda ya faru da misalin karfe 10 na daren Juma’a 26 ga watan Satumba.

Wani da abin ya faru a gaban idanunsa ya fadawa littafin cewa margayan suna wurin da bai dace ba a lokacin da bai dace ba, saboda ‘yan bindingar sun zo ne suna neman gidajen masu hannu da shuni a cikin al’umma lokacin da suka gamu da su.

An dai bayyana cewa an harbe su ne kafin su sace malamin a yankin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *