fbpx
Monday, September 27
Shadow

Yan bindiga sun kashe mutum shida, tare da raunata wasu a jihar Sokoto

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne yayin guduwa daga haren haren soji da ke gudana a jihar Zamfara sun kashe mutane shida tare da yin garkuwa da wasu a karamar hukumar Tureta ta jihar Sokoto.

Karamar hukumar Tureta tana da iyaka da jihar Zamfara inda aikin soji ke gudana.

An sanar da cewa bayan farmakin da ‘yan bindigar suka yi, mutane da dama sun ji rauni kuma yanzu haka suna karbar magani a asibiti.

A cewar majiyar, ‘yan bindigar sun kai farmakin ne da misalin karfe biyu na safiyar ranar Alhamis.

Majiyar ta yi bayanin cewa maharan sun yi kira sallah dan su yaudari ‘yan uwa don jawo hankalin mutane zuwa gare su.

A cewar majiyar, “Mazauna garin sun fara fitowa, suna tunanin lokacin sallar Asuba ne sai‘ yan bindigar suka fara harbin su. ”

Alhaji Maniru Dan’iya, mataimakin gwamnan jihar Sokoto ya ziyarci yankin tare da basu tabbacin jajircewar gwamnati na kawo karshen yan bindiga a jihar.

Mataimakin gwamnan ya kuma ba da tabbacin cewa gwamnatin jihar za ta biya dukkan kudaden mutanen da suka jikkata.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *