fbpx
Saturday, June 19
Shadow

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutune Biyu Tare Da Raunata Wasu Da Dama A Jihar Katsina

‘Yan bindiga sun kashe mutane biyu da raunata wasu a garin Bugaje dake karamar hukumar Jibiya a jihar Katsina.

 

Kamar yadda wakilinmu ya zanta da wani mazaunin garin, ya shaida yadda lamarin ya faru wajen Karfe 9:00 na daren jiya, ‘yan bindigar suka shigo garin yayin da suka ringa harbe-harbe wanda ya yi sanadiyar rasuwa mutane biyun.

 

“Dama a kwanakin baya ‘yan bindigar sun shigo garin inda suka ce sai an hada musu miliyan biyu matukar muna son su bar mu mu yi noma a wannan damunar”, inji shi.

 

Ta bangare gwamnatin jihar kuma har lokacin da muke hada wannan rahoto ba ta yi wani magana ba kan lamarin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *