fbpx
Saturday, October 16
Shadow

Yan bindiga sun kashe shugaban Miyetti Allah na karamar hukumar Lere a jihar Kaduna

Yan bindiga sun kashe Abubakar Abdullahi, shugaban kungiyar Miyetti Allah na karamar hukumar Lere ta jihar Kaduna.

Harin ya faru ne da sanyin safiyar Juma’a, Daraktan Watsa Labarai na MACBN a jihar Kaduna, Ibrahim Bayero-Zango, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai, duk da cewa babu wata sanarwa daga jihar ko kuma ‘yan sanda.

A cewar mai magana da yawun MACBAN, maharan sun kai hari gidan shugaban, wanda aka fi sani da Dambardi, a garin Lere da misalin karfe 1:00 na safe.

Ya kara da cewa ‘yan bindigar sun nemi N20m daga gare shi kafin a dauke shi zuwa inda maharan suka kashe shi a kan babbar hanyar Saminaka zuwa Mariri zuwa Zango.

“Duk da cewa ya iya basu Naira 250,000 ga maharan, amma sun kai shi bayan garin a kan babbar hanyar Saminaka zuwa Mariri zuwa Zango inda suka harbe shi har lahira.”

Kakakin MACBAN, yayin da yake yin Allah wadai da harin, yayi kira ga gwamnatin jihar da hukumar tsaro da su binciki harin domin gano wadanda suka aikata wannan danyen aikin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *