fbpx
Thursday, September 23
Shadow

Yan bindiga sun kashe sojoji 10, tare da yan sanda 2 yayin wani hari da suka kai sansanin sojoji a jihar

Awanni bayan gwamnan Zamfara, Bello Matawalle ya yi ikirarin cewa ‘yan bindiga na neman afuwa,’ yan bindigan sun kai hari kan sansanin sojoji da ke jihar, inda suka kashe a kalla jami’an 12 sannan suka jikkata wasu.

An tattaro cewa yan bindigan sun kai farmakin ne a garin Mutumji dake karamar hukumar Dansadau a jihar a ranar Asabar.

Sansanin sojojin yana da tazarar kilomita 80 kudu da Gusau babban birnin jihar.

An gano cewa mutane 12 da suka mutu sun hada da jami’an sojin saman Najeriya tara, ‘yan sanda biyu, da kuma wani sojan Najeriya guda daya.

‘Yan bindigar sun kuma kwace makamai daga ma’aikatan da aka kashe tare da kona kayan aiki a wurin.

Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) a makon da ya gabata ta umarci duk masu aikin sadarwa a jihar da su dakatar da ayyukansu a Zamfara, daga ranar Juma’a 3 ga Satumba, 2021.

“Su (yan bindiga) sun aika da kwamiti mai karfi don rokon mu da mu tsagaita wuta kuma mu ba da damar wadata (abinci da sauran muhimman kayayyaki) amma na ki,” in ji gwamnan. Gwamna Matawalle ya fada a ranar Juma’a bayan halartar sallar Juma’a a Masallacin Dalala a Gusau, babban birnin jihar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *