fbpx
Sunday, September 26
Shadow

Yan bindiga sun kashe wani soja tare da sace wata mata da yaranta a Zaria

Yan bindigar sun kai hari gidan wani ma’aikacin Jami’ar Jihar Kaduna (KASU), Dakta Ahmed Buba, a gidansa da ke unguwar Milgoma, daura da Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello, Shika Zaria. Sun yi garkuwa da mutane hudu a cikin al’umma.

An kashe jami’in sojan, Okekechukwu Ebuka, wanda yayi yunkurin kubutar da wadanda yan bindigan suka sace.

Mummunan lamarin ya faru ne a ranar 13 ga Satumba da misalin karfe 9.00 na dare, amma an yi nasarar kama ‘yan bindigar da sanyin safiyar ranar 14 ga Satumba, 2021, a Kasuwar Da’a da ke kan hanyar Birnin Gwari.

Wata majiya ta ce ‘yan bindigan sun kai kimanin 30, dauke da manyan makamai, sun ta harbe-harbe a sama yayin da suke farma al’umma.

Majiyar ta ce, “Hadin gwiwar ma’aikatan sa -ido na jihar Kaduna, sojoji da‘ yan sanda sun amsa kiran gaggawa. ”

A cewar majiyar, yayin da suka ga jami’an tsaro, ‘yan bindigar sun bude wuta tare da yin artabu da su, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar soja daya da kuma adadin wasu da suka jikkata.

Wani mazaunin yankin ya ce an kubutar da yara shida da aka sace a Kasuwan Da’a da ke karamar hukumar Zariya ta hanyar hadin gwiwar jami’an tsaro.

Ya kara da cewa yan bindigan sun tsere tare da matar gida daya, Rabi Isya da ‘ya’yanta- Sulaiman Isya, Amina Isiya da Mus’ab Isya.

Mukaddashin Mataimakin Darakta, Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar sojojin Nigeria, Zaria, ya ce ya samu labarin mutuwar sojan.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *