fbpx
Saturday, April 17
Shadow

Yan Bindiga Sun Kashe Wasu Manoma Uku a Jihar Taraba

Wasu ‘yan bindiga sun kashe wasu manoma uku a karamar hukumar Wukari da ke jihar Taraba.
Harin ya faru ne da sanyin safiyar ranar Laraba a kauyen Assa da ke wajen karamar hukumar Wukari.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga gidan talabijin na Channels ta wayar tarho, Shugaban majalisar, Adi Daniel, ya ce maharan sun zo ne da yawansu ta hanyar daji kuma sun shirya tashin hankalin.
Daniel ya lura cewa wasu manoma biyar da suka tsere daga harin sun samu munanan raunuka kuma a yanzu haka suna karbar kulawa a Babban Asibitin Wukari, ya kara da cewa manoman suna zaune a filin gonarsu lokacin da aka kai musu harin ba gaira ba dalili.
Wannan harin na zuwa ne kimanin awanni 24 bayan an kashe ‘yan sanda biyu a wani shingen binciken ababen hawa na Dogon-Gawa, wani yanki na karamar hukumar Takum wanda shi ma yana yankin Kudu na jihar Taraba.
Har yanzu ‘yan sanda ba su tabbatar da faruwar lamarin ba duk da cewa suna ikirarin har yanzu suna tsammanin cikakken bayani game da mummunan lamarin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *