fbpx
Thursday, August 5
Shadow

Yan bindiga sun kashe‘ yan sanda uku da wasu biyu a Anambra

Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kashe‘ yan sanda uku da wasu mutum biyu a garin Eke-Agu da ke Abatete, karamar hukumar Idemili ta Arewa a jihar Anambra.

A cewar rahotanni, ‘yan bindigan sun afka wa al’ummar ne a cikin manyan motoci biyu kirar SUVs da mota Sienna a daren Talata 13 ga watan Yuli, suna harbi lokaci-lokaci yayin da suka kuma kona motoci uku.

Maharan sun sace wani saurayi da ba a san ko waye ba daga Uke bayan harbin bindinga bai ratsa jikinsa ba.

Dagan suka sa shi a mota sukai awon gaba da shi zuwan wani wurin da ba’a sani ba.

Har yanzu rundunar ‘yan sandan jihar ba ta ce komai game da lamarin ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *