fbpx
Sunday, September 19
Shadow

Yan bindiga sun kwashe makudan kudade biyan ma’aikatan a jihar Nasarawa

Wasu ‘yan bindiga sun yi wa ma’aikatan Ma’aikatar Kudi, Kasafin Kudi da Tsare-Tsare ta Jihar Nasarawa fashin kudi N100m.

Wani ganau, wanda ya nemi a sakaya sunansa a ranar Alhamis, ya fada wa manema labarai cewa wadanda ake zargin ’yan fashi da makami ne sun bi jami’an ma’aikatar daga wani bankin kasuwanci da ke Lafia inda suka ciro kudi domin biyan ma’aikatan ma’aikatar.

Lamarin, a cewar shaidan, ya faru ne a ranar Talata a Lafia a harabar ma’aikatar, kusa da ofishin Akanta Janar na jihar, inda yawancin jami’an tsaro ke gadin babban Akanta Janar na jihar.

Majiyar ta ce, “A cikin harabar ma’aikatar ne masu dauke da muggan makamai suka kwace kudin, wanda muka ji labarin ya kai kimanin N100m, daga jami’an Ma’aikatar Kudin yayin da suke kokarin kwashe kudin daga motar kudin zuwa daki.

“A yayin fashin kudin,‘ yan bindigar suka yi ta harbi a iska lokaci-lokaci, wanda hakan ya sa jami’an ma’aikatar da ke dauke da kudin da sauran ma’aikatan ma’aikatar a cikin gida suka yi kasa, wanda ya bude wa ‘yan bindigar hanya don su tafi da kudin ba tare wani kalubale ba .

Majiyar ta kara da cewa “Jami’an ma’aikatar ba za su so kashe kudaden ma’aikatar a kan jami’an tsaro ba saboda haka sun yi watsi da ayyukan jami’an tsaro a harkokin yau da kullum na ma’aikatar,”

Lokacin da aka tuntubi Kwamishinan Kudi, Kasafin Kudi da Tsare-Tsare na jihar, Haruna Ogbole, ya tabbatar da faruwar lamarin amma ya ce ana ci gaba da bincike.

Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda a jihar, Ramhan Nansel, ya ce har yanzu rundunar ba ta samu cikakken bayani a kan lamarin fashin ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *