fbpx
Friday, May 14
Shadow

‘Yan Bindiga sun lalata Babbar Kotun Ebonyi, Sun kashe sojoji 2

‘Yan Bindiga sun kaiwa babbar kotun gwamnatin tarayya dake Abakaliki a Jihar Ebonyi hari inda suka banka mata wuta.

 

Lamarin ya farune da safiyar ranar Talata. Sun kona bangaren dakin ajiyar Litattafai da kuma dakin masu gadi.

 

A wani harin kuma da ‘yan Bindigar suka kai a Amasiri da Afikfo na jihar daidai wani shingen sojoji, sun kashe sojojin guda biyu.

 

Hakanan sun kuma kashe me gadin wani gidan sayar da Gas. Wannan harin sun kaishine da misalin karfe 9 na daren Litinin.

 

Sun kwashe makaman sojojin suka yi awon gaba dasu, kamar yanda Leadership ta ruwaito.

 

 

 

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *