fbpx
Friday, April 23
Shadow

Yan Bindiga Sun Nemi Kudin Kariya Na Miliyan N10 Daga Al’ummar Katsina Don Daina Ci Gaba Da Kai Hare-Hare

Biyo bayan harin da aka kai a kauyen Kakumi da ke karamar hukumar Bakori a cikin jihar Katsina, ‘yan fashin sun umarci al’umma su samar da Naira miliyan 10 a matsayin kudin kariya don dakatar da ci gaba da kai hare-hare.
A cewar Blueinknews, ‘yan bindigar sun aike da bukatarsu ta lambar wayar da suka kwace yayin wani hari da suka kai kauyen a ranar Juma’a.
Wani shugaban al’umma a yankin wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce ‘yan fashin sun bayyana cewa biyan wannan makudan kudade zai sa su daina kai hari a kauyen.
‘Yan bindigan sun kai hari a ranar Juma’a da misalin karfe 7:00 na dare suka far wa kauyen Kakumi inda suka kashe mutane uku tare da raunata wasu da dama.
Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan wasu ‘yan bindiga sun afkawa mazauna kauyen Dunkawa a karamar hukumar Sabon Birni da ke jihar Sokoto cewa ba za su daina kai hari ga al’ummomin yankin ba har sai gwamnati ta yi musu afuwa tare da biyansu alawus-alawus duk wata.
SaharaReporters ta tattaro cewa yan bindigan wadanda suka afkawa kauyen dauke da manyan makamai a ranar Alhamis sun yi alfahari cewa babu wanda zai iya taimakawa mazauna yankin sai dai idan an biya musu bukatunsu.
An samu labarin cewa sun shigo kauyen ne, dauke da manyan makamai tare da rera taken daban-daban.
A cewar mazauna, sun yi yawo ba tare da kulawa ba, suna yawo harda siyan kayan a shagunan yankin.
“Sun ce mana kar mu firgita tunda ba su cikin al’umma don su kawo hari ko kashe wani sai dai su tura mu zuwa ga gwamnati. Sun ce ba wanda, hatta Shugaban kasa, Muhammadu Buhari da zai iya taimaka mana har sai gwamnati ta yi musu afuwa kuma ta amince za ta biya su alawus-alawus duk wata.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *