fbpx
Friday, January 21
Shadow

‘Yan Bindiga sun sace babban dan siyasa a Arewa, sun nemi Miliyan 50

‘Yan Bindiga sun sace tsohon dan takarar gwamnan jihar Filato, Nkemi Nicholas Nke inda suka nemi a biya kudin fansa Miyan 50.

 

An saceshi ne daga gidansa a ranar Asabar, Nshe ya taba yin shugaban karamar hukumar Shendam sannan kuma yayi takarar neman gwamna a shekarar 2019.

 

Hakan na zuwane kwanaki kadan bayan sace wani basaraken da aka yi a Jos din inda aka nemi Naira Miliyan 500.

 

Wani na kusa da dan siyasar ya tabbarwa da Punchng faruwar lamarin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *