fbpx
Friday, May 14
Shadow

Yan Bindiga Sun Sace Babban Jami’in Kula da Karamar Hukuma a Jihar Ekiti

Wasu ‘yan bindiga sun sace wani mai kula da karamar hukuma a jihar Ekiti.

Wannan na zuwa ne mako guda bayan da wasu ‘yan bindiga suka sace wani sarki suka mamaye fadarsa.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda a jihar, Sunday Abutu ya tabbatar wa gidan talabijin na Channels cewa an yi garkuwa da Sufetan na Karamar Hukumar ta Ekiti ta Yamma da yammacin Alhamis a lokacin da yake tuki zuwa wani gari cikin karamar hukumar (Erijiyan Ekiti).
An bayar da rahoton cewa an bar motarsa ​​a gefen hanya yayin da masu satar suka tafi da shi.
Abutu ya bayar da tabbacin cewa rundunar ‘yan sanda ta jihar za ta tabbatar da kubutar da dan siyasan da kuma ci gaba da kokarin kawar da masu satar mutane da sauran masu laifi a jihar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *