fbpx
Saturday, October 16
Shadow

Yan bindiga sun sace babban ma’aikacin gwamnati

Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da Babban Sakataren Ma’aikatar Sufuri ta Jihar Neja, Dakta Ibrahim Garba Musa, tare da jikarsa.

An samu labarin cewa an sace Musa ne a gidansa da ke Zungeru, inda ya je bikin aure. ‘Yan bindigar sun dauke shi ne cikin dare bayan biki.

Daya daga cikin dangin ya ba da labarin cewa ‘yan bindigar sun shiga gidan ta hanyar fasa kofa don yin garkuwa da Babban Sakataren wanda ke shakatawa bayan bikin.

Ya kara da cewa tuni dangin sun tuntubi gwamnatin jihar domin sanar da su abin da ya faru.

Sakataren gwamnatin jihar Neja, Ahmed Ibrahim Matane, lokacin da aka tuntubi shi, ya ce an sanar da shi faruwar lamarin amma har yanzu bai tabbatar da hakan ba.

Ya ce, duk da haka, gwamnatin jihar za ta yi iya bakin kokarinta don ganin an kubutar da Babban Sakataren ba tare da lahani ba.

Kokarin jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Neja, DSP Abiodun Wasiu, ya ci tura har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *