fbpx
Saturday, October 16
Shadow

Yan bindiga sun sace babban sakatare a ma’aikatar sufuri ta Nijar da dansa

Wasu da ake zargin yan bindiga ne sun sace Ibrahim Garba Musa, babban sakatare a ma’aikatar sufuri ta Nijar.

An yi garkuwa da shi da sanyin safiyar ranar Asabar, 2 ga watan Oktoba tare da dansa a yankin Zungeru na jihar, inda suka je bikin aure.

Mary Noel-Berje, babban sakataren yada labarai na gwamnan jihar Abubakar Sani Bello, ta tabbatar da faruwar lamarin.

Ta ce gwamnan ya kuma “yi tir da munanan ayyukan yan bindiga a kananan hukumomin Shiroro da Munya kwanan nan, inda aka yanka mutane da yawa, aka kona wasu aka yi garkuwa da su ”.

Sace shi na zuwa ne watanni biyu kacal bayan wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka sace Sani Idris, kwamishinan yada labarai na jihar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *