fbpx
Monday, September 27
Shadow

‘Yan Bindiga sun sace dalibai da yawa a jihar Zamfara

Rahotanni daga jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya sun ce ‘yan bindiga sun kai hari wata makarantar maza da mata da ke karamar hukumar Maradun kuma sun sace dalibai da dama.

Mazauna garin Kayan Maradun sun shaida wa BBC Hausa cewa ‘yan bindigar sun kai harin ne da safiyar Laraba kuma sun sace daliban da ya zuwa yanzu ba a kai ga sanin adadinsu ba.

Rahotanni sun ce dalibai fiye da 400 ne suke makarantar lokacin da aka kai harin suna masu karawa da cewa daliban suna rubuta jarrabawar ‘Mock’ ta ‘yan aji biyar ne lokacin da aka kai harin.

Wani malamin makarantar ya shaida mana cewa lamari ya faru ne “muna shirye-shiryen yin jarrabawar mock ta ‘yan aji biyar, bayan mun fito mun yi wa ‘yan SS II bayani mun fito mun tunkaro dakin malamai, muna zaunawa sai kawai muka ji kukan babura sun tunkaro makaranta.”

A cewarsa, daga nan ne suka watse suka shiga cikin gonar gero tare da wasu daliban amma duk da haka ‘yan bindigar sun kwashe dalibai da dama.

Sai dai kawo yanzu hukumomi ba su tabbatar da adadin daliban da aka sace ba.

Amma malamin ya ce daliban da ke makarantar suna da yawa sosai lokacin da maharan suka shiga.

Wannan lamari na faruwa ne kwanaki kadan bayan gwamnatin jihar Zamfara ta dauki wasu sabbin matakai na kawo karshen hare-haren ‘yan bindiga.

Matakan sun hada da hana bude kasuwannin da ke ci mako-mako da takaita yawan man fetur din da za a sayar da sauransu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *