fbpx
Monday, May 10
Shadow

Yan bindiga sun sace farfesan Jami’ar Ambrose Alli, sun nemi kudin fansa N18m

Wasu ‘yan bindiga sun sace wani malami a jami’ar Ambrose Alli (AAU), Ekpoma, jihar Edo, Farfesa Osadolor Odia.

Odia, Farfesa ne bangaren Kimiyya da kere-kere kuma tsohon Shugaban Sashin Injiniyanci, an sace shi ne a kan hanyarsa ta zuwa gona a Egoro, Ekpoma, a karamar Hukumar Esan West da safiyar Alhamis, 29 ga Afrilu.

Wata majiya, wacce ta nemi a sakaya sunanta ta shaida wa manema labarai cewa masu garkuwan sun tuntubi dangin suna neman kudin fansa na Naira miliyan 18.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *