fbpx
Saturday, December 4
Shadow

Yan bindiga sun sace hakimin Banye a jihar Katsina

An gano cewa an sace hakimin kauyen Banye na karamar hukumar Charanci, Alhaji Bishir Gide Banye tare da wani dalibin sakandare.

Wani mazaunin garin, wanda ya shaida wa manema labarai, ya tabbatar da cewa maharan dauke da muggan makamai sun mamaye garin a daren Juma’a sannan suka tafi kai tsaye zuwa fadar hakimin inda suka sace shi tare da dayan wanda aka sacen.

Wannan shi ne karo na biyu da aka sace wani hakimin kauyen a yankin, kamar yadda aka yi garkuwa da hakimin garin Barkiya da ke karamar hukumar Kurfi.

Amma ya yi sa’ar samun ceto yayin da aka sanar da jami’an tsaro sannan suka hanzarta bin sawun masu garkuwa da mutanen.

Lokacin da aka tuntube shi don tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sanda a Katsina, SP Gambo Isah, ya ce rahoton bai kai ga hedikwatar rundunar ba amma ya yi alkawarin ganowa da bada rahoto.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *