fbpx
Tuesday, June 15
Shadow

Yan bindiga sun sace Hakimin Zungeru da matansa biyu a jihar Neja

Hakimin tsohon garin Zungeru a karamar hukumar Wushishi, na jihar Neja, Malam Mustapha Madaki, (Madakin Zungeru), da matansa biyu ana zargin ‘yan bindiga sun sace su.
An tattaro cewa yan bindiga kimanin 20, sun isa Zungeru da misalin 1:40 na safiyar Lahadi kuma suka nufi gidan Madakin Zungeru wanda yake a tsakiyar garin.
An ce sun kama shi daga dakin daya daga cikin matan, Habiba kuma suka tafi da shi tare da matansa biyu.
Wata majiya daga yankin ta shaida cewa ’yan bindigan sun isa yankin kuma suka tafi kai tsaye gidan Madaki suka dauke shi shi da matansa.
Majiyar ta bayyana cewa, “harin daga abin da muka gani an aiwatar da shi ne ta hanyar wani mai ba da rahoto saboda kawai hakimin da matansa ne aka sace daga garin a wani aiki da ya dauki tsawon mintuna 30 kawai ba tare da wata turjiya daga ko’ina ba”
An kuma tattaro cewa yan fashin basu tuntubi dangin wadanda lamarin ya shafa ba.
Kokarin jin ta bakin rundunar ‘yan sanda na jihar ya ci tura saboda jami’in hulda da jama’a PRO, DSP Wasiu Abiodun bai samu ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *