fbpx
Sunday, September 19
Shadow

Yan bindiga sun sace jigon PDP na Edo

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace Pa Owere Dickson Imasogie, wani jigo a jam’iyyar PDP a gundumar sanatan Edo ta Kudu.

An ce an yi garkuwa da shi tare da direbansa da wani mutum, wanda ba a tantance ko su wanene ba, a babbar hanyar Benin zuwa Agbor a safiyar ranar Litinin, 13 ga watan Satumba.

An tattaro cewa Pa Imasogie na kan hanyarsa ta zuwa daya daga cikin gonakinsa lokacin da ‘yan bindigar suka kai harin.

Wata kungiya da aka fi sani da ” Edo State Decide Movement ” ta tabbatar da sace mutanen a cikin wata sanarwa kuma ta bukaci Gwamna Godwin Obaseki, cikin gaggawa, “ya dauki kwararan matakai don ganin an ceto shi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *