fbpx
Monday, September 27
Shadow

Yan bindiga sun sace kanwar mataimakin kakakin majalisar Katsina da ke shirin yin aure

Yan bindiga sun sace kanwar Hon. Shehu Dalhatu Tafoki, Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Katsina.

An bayyana cewa ‘yan bindigan sun kai hari kauyen Tafoki da ke karamar hukumar Faskari a jihar a ranar Lahadi, 5 ga watan Satumba, inda suka yi garkuwa da mai suna Asma’u Dalhatu.

Dan majalisar ya tabbatar wa Aminiya faruwar lamarin, inda ya kara da cewa ‘yar uwarsa na gab da yin aure, kuma sun sace wata yarinya.

Ya kuma ce; A kan hanyar yan bindingar zuwa dajin, sun ci karo da wasu‘ yan kungiyar ’yan banga kuma sun yi musayar wuta.

Ana cikin haka sai daya daga cikin ‘yan matan ta tsere ta koma gida, amma dayar (yar uwarsa) ba ta iya guduwa, don haka suka tafi da ita.

Tafoki ya ce har yanzu masu garkuwar ba su nemi kudin fansa ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *