fbpx
Friday, May 14
Shadow

‘Yan Bindiga sun sace mata 20 da suka je bikin Suna a Katsina

Kimanin Mata ashirin ne aka sace a kauyen Gidan Bido dake karamar hukumar Dandume a jihar Katsina, a lokacin da suka je kauyen domin halartar bikin suna a jiya Juma’a.

Majiyar RARIYA ta tabbatar mata cewa yan bindigar sun zo ne da misalin karfe dayan daren jiya Juma’a dauke da manyan bindigogi, suka sace matan.

Haka zalika, yan bindigar sun kai makamanci irin wannan harin a mahaifar dan Majalisar jihar, mai wakiltar karamar hukumar Dandume a majalisar dokoki ta jihar Katsina, Honarabul Haruna Goma, watau Unguwar Bawa, inda suka sace maza guda biyar duk a daren jiya.

Daga Jamilu Dabawa, Katsina

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *