fbpx
Wednesday, January 26
Shadow

‘Yan bindiga sun sace mutum 12 ciki har da mata 10 a Kaduna

Akalla mutum 12 ne ciki har da mata 10 wadanda ‘yan bindiga suka sace a karamar hukumar Giwa da ke jihar Kaduna a arewacin Najeriya a safiyar Juma’a.

Shugaban matasan kauyan Jamil Kerawa ya tabbatar da shigar ‘yan bindigar wadanda suka yi abin da suka ga dama ba tare da an kalubalance su ba kamar yadda ya shaida wa jaridar DailyTrust.

“Sun sace mutane 12 biyu daga cikinsu maza ne sauran kuma mata bayan sun kashe mutum guda.

“An kuma ji wa wani rauni kuma tuni aka garzaya da shi asibitin da ke Zaria.

Muna matukar bukatar taimako a nan, ubangiji ne ke kare mu.” in ji shi.

Ya nemi gwanati da takai ‘yan sanda yankin nasu domin basu kariya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *