fbpx
Saturday, June 19
Shadow

Yan Bindiga Sun Sace Shanu 500 A Cikin Al’umman Jihar Kebbi

A ranar Lahadin da ta gabata, tan bindiga sun saci shanu 500 a karamar hukumar Sakaba ta jihar Kebbi.

Shugaban kungiyar ‘yan banga a masarautar Zuru, John Mani ne ya bayyana hakan a ranar Litinin, yayin da yake tattaunawa da Aminiya ta wayar tarho.

Ya ce fitattun ‘yan bindigar sun addabi al’ummar masarautar a cikin’ yan makonnin da suka gabata.

Sakaba na daya daga cikin kananan hukumomi hudu da suka hade da masarautar Zuru.

A cewarsa, ‘yan ta’addan wadanda galibi ke shigowa cikin jihar ta kan iyakokin kebbi da Zamfara da Kebbi da Neja, sun mamaye garuruwan ne da rana tsaka suka kwashe shanun.

Game da ko an kashe wasu mutanen gari, Mani ya ce ba a rasa rai ba yayin da maharan da suka mamaye garuruwan suka zo kan babura sama da 500, inda kowannensu ke dauke da mutum biyu.
Ya ce, “’ Yan bindiga daga Zamfara da Neja sun mamaye wasu garuruwa a karamar Hukumar Sakaba da ke Jihar Kebbi inda suka sace shanun.

“A kowace garken, akwai shanu 100. Ba a rasa rai ba saboda kawai sun auna shanu ne. ”
Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar, DSP Nafiu Abubakar, bai dauki kiran wayarsa ba.
Hakanan, bai amsa sakon tes da aka aika masa ba a lokacin rubuta wannan rahoton.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *