fbpx
Wednesday, May 12
Shadow

‘Yan Bindiga sun sace Shugaban karamar Hukuma a jihar Kogi

An sace shugaban karamar hukumar Yagba ta yamma na jihar Kogi, Mista Pius Kolawole.
An yi garkuwa da Kolawole ne a kan hanyarsa daga Ilorin, babban birnin jihar Kwara zuwa garinsa na haihuwa Egbe, garin kan iyaka tsakanin Kogi da jihar Kwara.
Sai dai, Kwamishinan Hukumar Fensho na Jihar, Mista Solomon Adegbayo, wanda aka fi sani da Akeweje, wanda suke cikin mota daya tare da shugaban bai yi sa’a ba saboda masu satar sun harbe shi.
A halin yanzu, rundunar ‘yan sanda reshen jihar Kogi ta ce ta fara neman inda Shugaban Yagba na Yamma yake.
Jaridar Vanguard ta tattaro cewa an kashe marigayi Solomon Akeweje ne da yammacin ranar Asabar da wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba a cikin motarsa ​​a Eruku wasu ‘yan kilomitoci zuwa Egbe yayin da yake dawowa daga Ilorin jihar Kwara.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kogi, (PPRO), DSP William Aya wanda ya tabbatar da faruwar lamarin yayin wata tattaunawa da Lokoja a ranar Lahadi ya ce Kolawole na tare da Akeweje a cikin mota daya lokacin da‘ yan bindiga suka far musu a Eruku.
Aya ya ce harsashin bindiga ya sami Akeweje kuma ya mutu.
Ya kara da cewa an ijiye gawar sa a asibitin ECWA, Egbe yayin da ba a san inda Kolawole ya ke ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *