fbpx
Sunday, September 19
Shadow

Yan bindiga sun sace tsohon dan majalisar PDP a Jigawa, tare da kashe wani mutum

asu ‘yan bindiga sun yi awon gaba da wani tsohon dan majalisar dokokin jihar Jigawa mai wakiltar mazabar Auyo, Hon. Haladu Bako Uza.

An tattaro cewa an sace tsohon dan majalisar a hanyar Kano zuwa Hadejia a daren Laraba.

An yi garkuwa da shi ne a kan hanyarsa ta zuwa mahaifarsa, Auyo, daga jihar Kano.

Dan majalisar ya wakilci mazabar Auyo a majalisar jihar daga 2007 zuwa 2015 a karkashin inuwar People’s Democratic Party, PDP.

Kakakin ‘yan sanda, ASP Lawan Shiisu Adam, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce lamarin ya faru ne lokacin da ‘yan bindigar, wadanda yawansu ya kai biyar, suka tare Ringim zuwa garin Gujungu tare da yi wa masu motoci fashi. Ya bayyana cewa ‘yan fashin sun harbe wani direban mota a yayin aikin.

Adam ya ce ‘yan sanda sun garzaya zuwa wurin bayan kiran da aka yi musu na gaggawa kuma sun gano harsasai. Ya kara da cewa an hada runduna ta sintiri don ceto wanda lamarin ya rutsa da shi tare da cafke masu laifin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *