fbpx
Saturday, October 16
Shadow

Yan bindiga sun sace uwa da ‘yarta a Jihar Adamawa

Wasu ‘yan bindiga sun kai wa ofishin ‘yan sanda hari a Yola babban birnin Jihar Adamawa sannan suka sace wata mata da ‘yarta.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Sulaiman Nguroje, shi ne ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a yau Lahadi.

A cewarsa, maharan sun far wa ofishin da misalin ƙarfe 2:00 na daren Lahadi amma babu wanda ya ji rauni ko kuma kisa.

“Maharan sun kai wa gidan Alhaji Umaru hari da ke Nasarawa B, Ƙaramar Hukumar Yola ta Kudu,” in ji shi kamar yadda kamfanin labarai na NAN ya ruwaito. “Sun rabu gida biyu don su ɗauke hankalin ‘yan sanda.

“Yayin da wasu ke kai wa gidan Alhaji Umaru hari suka ɗauki matarsa da ‘yarsa, sai wasu suka kai wa ofishin ‘yan sanda hari.”

Ya ƙara da cewa Kwamashinan ‘Yan Sanda Mohammed Barde ya bayar da umarnin tura dakaru ciki har da na kwantar da tarzoma zuwa yankin na Nguroje don bin sahun maharan.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *