fbpx
Thursday, May 6
Shadow

Yan bindiga sun sace wani basaraken gargajiya a Jihar Ekiti

Idan zaku tuna a bayan Elewu na Ewu, Oba Adetutu Ajayi dake a cikin ƙaramar Hukumar Ilemeje ta Jihar Ekiti, ya ketare rijiya da baya daga masu satar mutane, sai dai Oba David Oyewumi na Obadu na Ilemeso-Ekiti dake cikin karamar Oye bai yi sa’a ba.

Domin kuwa, ‘Yan bindiga sun yi awon gaba da shi (Oba Oyewumi) a fadarsa inda suka tsallaka ta katanga, suka yi ta harbe-harbe a sama kafin su wuce da shi.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda, rundunar’ yan sanda ta jihar Ekiti, Mista Sunday Abutu, ya ce “lamarin ya faru ne jiya a fadarsa”.

Abutu ya ci gaba da cewa an dauki matakan da suka dace don kubutar da Masarautar da kuma cafke masu laifin.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoton, ba a ji komai daga masu garkuwar ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *