fbpx
Monday, September 27
Shadow

Yan bindiga sun sace wani Hakimin a jihar Neja

An yi garkuwa da Hakimin Wawa a masarautar Borgu ta jihar Neja, Alhaji Mahmud Ahmed Aliyu.

Hakimin da aka fi sani da Dodo na Wawa wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun sace shi daga fadarsa a daren Asabar.

An tattaro cewa ‘yan bindigar dauke da muggan makamai sun kutsa kai cikin fadar Hakimin da misalin karfe 10 na dare sannan suka fara harbi ba zato ba tsammani wanda ya haifar da fargaba a cikin fadar da daukacin al’umma.

A cikin rudanin da ya biyo baya, an sace basaraken.

Wata majiya ta ce ‘yan bindigar sun tafi da Alhaji Aliyu ta cikin dajin Kainji, zuwa Jamhuriyar Benin.

Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun ya tabbatar da faruwar lamarin.

Abiodun ya ce an tura rundunar ‘yan sanda ta musamman don gano masu garkuwa da mutanen, yana mai tabbatar da cewa za a cafke su nan ba da jimawa ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *