fbpx
Tuesday, June 15
Shadow

Yan bindiga sun sace wani malamin Jami’ar jihar Filato, UNIJOS

Rahotanni sun ce wasu da ake zargin masu satar mutane ne sun sace Dr Dan Ella, malami a jami’ar Jos, jihar Filato.

Jaridar DAILY POST ta ruwaito cewa an sace malamin da ke sashen wasan kwaikwayo  a safiyar ranar Laraba.

An kuma tattaro cewa yan bindigan sun kai hari gidansa da ke Haske kwatas a garin Lamingo, karamar hukumar Jos ta Arewa a Filato.

Cikakken bayanin abin da ya faru har yanzu ba a gama samu ba a lokacin rubuta wannan rahoto saboda shugabannin Jami’ar ba su bayar da wata sanarwa game da abin da ya faru ba.

Amma, da aka tuntube shi, jami’in hulda da jama’a na ’yan sandan Jihar, PPRO, ASP Ubah Gabriel Ogaba ya shaida cewa ba su da masaniya game da lamarin.

“Ba mu san da wannan rahoton ba.”

Wannan na zuwa ne kasa da wata guda bayan wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba wadanda ake zargin masu satar mutane ne suka yi awon gaba da wani farfesa a Sashen Kimiyyar Microbiology na Jami’ar Jos, Grace Ayanbimpe da mijinta.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *