fbpx
Sunday, September 26
Shadow

Yan bindiga sun sace wani uba da dansa a Abuja

Wasu gungun ‘yan bindiga dauke da makamai sun yi garkuwa da wasu‘ yan gida daya, su biyu a Abuja ranar Juma’a.

Maharan sun kai hari ne a wani gida da ke kauyen Yangoji a karamar hukumar Kwali inda suka yi awon gaba da uba da dan sa.

Sun sace Abdullahi Benda da Jibrin Benda, mai shekaru 23, bayan mamaye gidan da sanyin safiya.

Wasu sun tsallake katangar gidan, suka fasa kofar, suka ja wadanda abin ya rutsa da su waje.

Da farko masu garkuwar sun yi kokarin tafiya da matar mai gidan amma sun bar ta bayan sun gano kwanan nan ta haifi jariri.

Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya (FCT) ta tabbatar da faruwar lamarin.

Jami’in hulda da jama’a ASP Daniel Ndirpaya, ya shaida cewa “rundunar na kokarin ceto wadanda lamarin ya rutsa da su”.

Yankunan Abaji, Bwari da Kwali suna fuskantar karuwar masu garkuwa da mutane sosai a yan kwanakin nan.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *