fbpx
Thursday, August 5
Shadow

Yan bindiga sun sace wani wani mutum dan shekara 38 a Jigawa

Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun sace wani mutum mai shekaru 38 a karamar hukumar Kiyawa da ke jihar Jigawa.

Wani mazaunin, wanda kuma dangin wanda aka sace din ne, Aliyu Zakar ya fada cewa gungun wasu masu aikata laifuka biyar sun tsallaka zuwa gidan mutumun a ranar Litinin suka tafi da shi.

Ya bayyana cewa ‘yan fashin sun tafi da shi tare da neman a ba su naira miliyan sittin wanda suke so a kawo masa a daren da ya faru.

Ya ce an yi wa gidan duka fashi sannan wayar wanda aka sace da ta matan nasa duk masu laifin sun tattara su, ya kara da cewa har yanzu ba su tuntubi dangin ba.

Kakakin ‘yan sanda, ASP Lawan Shiisu Adam ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce lamarin ya faru ne a rukunin gidajen Dankoli da ke karamar hukumar Kiyawa da misalin karfe 3:00 na safiyar Litinin.

Adam, ya ce rundunar tana kokarin ganin ta cafke wadanda ake zargin tare da kubutar da mutumin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *