fbpx
Wednesday, June 23
Shadow

Yan bindiga sun sace wata malamar makaranta a Abuja

Misis Daramola Onyeaka Matina  malamar Makarantar Sakandaren Gwamnati (GSS), Kuje, Abuja, wasu ‘yan bindiga sun sace ta

Majiyarmu ta labarta mana cewa lamarin ya faru ne a garin Shadadi da ke karamar hukumar Kuje a ranar Talata lokacin da ‘yan bindigar suka mamaye yankin suna harbi kafin sace malamar.

Wata majiya da ke kusa da malamar ta ce wadanda ake zargin masu garkuwar sun kutsa kai yankin, inda suka nufi malamar kawai.

Wani dan gidan ya kuma shaida wa manema labarai cewa wadanda suka sace ta sun kira dangin, inda suka bukaci a ba su Naira miliyan 10 a matsayin sharadin sakin wanda suka sace.

Lokacin da aka tuntube shi, jami’in hulda da jama’ar na ’yan sanda na FCT, ASP Maryam Yusuf, ta tabbatar da faruwar lamarin.

A cewar PPRO, rundunar ‘yan sanda ta FCT ta fara aiki don tabbatar da ceto wanda aka sacen ba tare da rauni ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *