fbpx
Wednesday, April 21
Shadow

Yan bindiga sun sake sace matafiya biyu a Osun

A yammacin ranar Asabar ne aka sace wasu matafiya a yankin Wasinmi, da ke kan babbar hanyar Ife zuwa Ibadan a cikin jihar Osun.

An bayyana cewa wadanda lamarin ya rutsa da su sun nufi yankin Ikire.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan Osun, SP Yemisi Opalola ta bayyana cewa‘ yan sanda sun tura jami’ansu zuwa wurin da abin ya faru.
Ta kuma bayyana cewa an cafke mutum uku wadanda ake zargi da hannu a satar, yayin da ‘yan sanda suka tsaurara neman wadanda aka sace.
Idan za a tuna cewa an sace wasu matafiya a ranar Talata, a hanyar dai ta Ibokun zuwa Osogbo a cikin jihar.
Daya an harbe shi har lahira, yayin da wasu biyu suka samu raunuka na harbin bindiga.
‘Yan sanda a karshen mako sun ba da sanarwar sakin matafiya bakwai da aka sace, suna masu cewa har yanzu jami’an tsaro na kan hanyar wadanda suka sace su.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *