fbpx
Wednesday, June 23
Shadow

‘Yan Bindiga sun shiga Abuja sun sace mutane 83

‘Yan Bindiga sun mayar da unguwannin talakawa dake babban birnin tarayya, Abuja wajan cin karensu ba babbaka.

 

Unguwannin da suke shiga sun hada da Abaji, Bwari, Gwagwalada, Kuje da Kwali. Mutane da dama sun bar gidajensu a yankin saboda fargabar matsalar tsaro.

 

Maharan sun kuma tilastawa mutane barin gidajensu a kauyukan dake kusa da babban birnin tarayya,  Abuja na jihohin Nasarawa da jihar Naija.

 

A tsakanin Watan Janairu zuwa 23 ga watan Mayu, Daily Trust ta ruwaito cewaz mutane 83 ne aka sace a Abuja.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *