fbpx
Monday, September 27
Shadow

‘Yan Bindiga sun shiga gida a Abuja sun sace mutane 3

‘Yan Bindiga sun shiga wani gida a Pegi dake Kuje a babban birnin tarayya Abuja inda suka sace wata mata me shekaru 45 da jikokinta 2.

 

Sunan matar da aka sace, Mrs Oladapo Bukola, kuma an sace ta ne yayin da mijinta baya nan.

 

Dama a baya an sace mahaifin yaran, Abdullahi Benda, da dansa, Jibrin Abdullahi Bende.

 

‘Yansanda sun tabbatar da faruwar lamarin inda suka ce suna kokarin kwato wanda aka sace din.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *