fbpx
Wednesday, October 20
Shadow

Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Motoci Guda Biyu Kirar Bas Cike Da Fasinjoji A Ciki A Jihar Katsina

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun yi garkuwa da wasu motoci guda biyu kirar bas cike da mutane a ciki a yammacin jiya Lahadi a karamar hukumar Batsari dake jihar Katsina.

An sace mutanen ne a hanyar su ta dawowa daga kasuwar garin Jibiya.
Majiyar ta rawaito cewa an sace mutanen ne a kauyen Gobirawa wanda ke da nisan kilomita biyar tsakaninsa da garin Batsari.
An kiyasin cewa mutanen dake cikin motocin sun kai su 38.
Saidai har zuwa lokacin hada wannan rahoto, rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ba ta tabbatar da aukuwar lamarin ba.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *