fbpx
Tuesday, August 3
Shadow

‘Yan Bindiga ya kamata ka yaka ba Nnamdi Kanu ba>>Col. Abubakar Umar ya gayawa shugaba Buhari

Gwamnan jihar Kaduna a lokacin mulkin Soja, Col. Abubakar Umar mai Murabus ya bayyana cewa, ‘yan Binya kamata shugaba Buhari ya yaka ba Nnamdi Kanu ba.

 

Yace kama Nnamdi Kanu ya kara jawo hankula kan abinda Kanun yake wanda kuma bai ma dace a mayar da hankali kanshi ba.

 

Yacs abin takaici ne yanda maimakon gwamnatin Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ta mayar da hankali kan magance matsalar tsaro, ta koma tana yakar Nnamdi Kanu da IPOB.

 

Yace ga ‘yan Arewa dake zaune a yankunan Arewa maso gabas da Arewa maso Yamma, kama Nnamdi Kanu babu abinda ya amfanesu dashi tunda bai kawo musu karshen tashe-tashen hankulan da suke fuskanta ba.

 

Ya bayyana hakane a wata sanarwa da ya fitar me taken Kalubalen kasa, kamar yanda Punchng ta ruwaito.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *