fbpx
Thursday, July 29
Shadow

Yan bindinga na Zamfara sun ‘yantar da mutane 100 wadanda suka yi garkuwa da su

Akalla mutane 100 da aka sace a kauyen Manawa, da ke karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara sun samu ‘yanci bayan sun kwashe kwanaki 42 a hannun masu garkuwar.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar ta Zamfara, CP Hussaini Rabiu, a lokacin da yake tabbatar da ci gaban, ya ce rundunar tare da hadin gwiwar Ma’aikatar Tsaro da Harkokin Cikin Gida ta tabbatar da sakin mutanen ba tare da wani sharadi ba.

CP Rabiu a cikin wata sanarwa daga jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda, SP Mohammed Shehu ya ambaci cewa an saki wadanda aka sace din ba tare da biyan ko sisi ba.

Shugaban ‘yan sanda ya ba da tabbacin amfani da hanyoyi daban-daban don kawo karshen matsalar yayin da ya gargadi’ yan ta’addan masu tayar da kayar baya da su guji aikata laifuka su rungumi zaman lafiya ko kuma su fuskanci fushin doka.

A karshe yayi kira ga mutanen kirki da su taimaka wa jami’an tsaro wajen basu bayanai game duk wani abu da ba su yarda da shi ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *