fbpx
Monday, September 27
Shadow

Yan bindinga sun nemi a basu shinkafa da taliya a matsayin kudin fansa bayan rufe wasu kasuwannin 

Yan bindinga a halin yanzu suna neman kayan abinci a matsayin kudin fansa a yankunan Sakkwato, bayan rufe kasuwanni da yawa a jihohi hudu na Arewa maso Yamma.

Wani mazaunin Sabo Birni, wanda ba’a bayyana sunansa ba, ya zanta da Aminiya inda yace yan bindinga sun saki yaron makwabcinsa bayan an kai kayan abinci a madadin kudin fansa.

Haka ma wani mazaunin Sakkwato ya shaida wa jaridar yadda ‘yan bindiga suka nemi kayan abinci da abin sha don sakin direban da suka sace.

Yace; Da farko sun nemi Naira miliyan 15 kafin daga baya suka amince su karbi N600,000.

“Sun cewa maigidan direban da ya yi amfani da kuɗin don siyo masu buhunan shinkafa, lemon sha, katan spaghetti da sigari ya kuma kawo musu sauran canji. Mutumin har yanzu yana kokarin tara wadannan kudaden.

Wani mai sharhi kan sha’anin tsaro, Aminu Bala Sokoto, ya ce lamarin ya nuna cewa hare -haren da sojoji ke kai wa ‘yan bindiga a Zamfara ne ya haifar da wannan mawuyancin hali da yan bindingar ke ciki.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *