fbpx
Monday, September 27
Shadow

Yan fashin teku sun yi garkuwa da matafiya biyar a Jihar Ribas

Wasu da ake zargin ‘yan fashin teku ne sun yi garkuwa da fasinjojin jirgin ruwa guda biyar a kan hanyoyin ruwan Bonny-Onne a jihar Ribas.

Shugaban, Kungiyar Ma’aikatan Ruwa ta Najeriya (MWUN), Bonny Unit, Henry Jumbo, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce ya samu kiran gaggawa cewa ‘yan bindigar sun kai wa jirgin ruwan fasinja hari.

Jumbo ya ce biyar daga cikin fasinjoji 18 na jirgin an yi garkuwa da su zuwa wani wurin da ba a sani ba a ranar Talata.

Ya yi kira ga hukumomin tsaro da su kafa sashin tsaro a tashar jiragen ruwa na Onne da hanyoyin ruwan Bonny don dakatar da kai hare -hare a kan hanya.

Ya kara da cewa masu garkuwar har yanzu ba su tuntubi kungiyar ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *