fbpx
Friday, May 14
Shadow

‘Yan Fim sun godewa Rarara saboda tallafin Miliyan 3

ƊIMBIN jama’a, musamman ma dai ‘yan fim, sun yaba wa fitaccen mawaƙi Dauda Adamu Kahutu (Rarara) saboda tallafin tsabar kuɗi har naira miliyan 3 da ya raba wa ‘yan fim 60 da ake ganin mabuƙata ne.

Idan kun tuna, Rarara ya raba kuɗin ne a makon jiya saboda rage wa ‘yan fim ɗin matsin da ake ciki a wannan wata na Ramadan.

‘Yan fim maza da mata ne su ka amfana da tallafin, inda aka ba kowannen su N50,000.

Wasu daga cikin waɗanda su ka ci moriyar tallafin sun bayyana farin cikin su ga mujallar Fim, kuma su ka yi wa Rarara fatan alheri.

Sun bayyana shi a matsayin wani jajirtaccen mutum mai amfani da damar sa wajen ganin ya taimaka wa mutanen da ba su da ƙarfi a cikin wannan masana’anta ta Kannywood.

Sai dai daga cikin waɗanda su ka amfana sun bayyana cewa wannan ba shi ne karo na farko da mawaƙin ke taimaka wa ‘yan fim ba.

A tattaunawar sa da mujallar Fim, dattijo Alhaji Isah Bello Ja wanda ya na ɗaya daga cikin waɗanda su ka amfana da tallafin, ya bayyana cewa tallafin ya zo a daidai lokacin da ake da buƙatar sa.

Ya ce, “Wannan tallafi ya zo a daidai lokacin da ake da buƙata. Haƙiƙanin gaskiya duk wanda aka ba wa tallafin nan ya na da buƙatar sa, duk da cewa ba wannan ne na  farko ba, don watanni biyu da su ka gabata ya bada tallafin dubu hamsin-hamsin ga wasu mutane, kuma har da ni a ciki, kuma wannan ɗin ma ya sake bada tallafin har da ni a ciki.

“Kun ga ban da mutumin kirki mai tsoron Allah, ko wanda ya ke neman gudunmawa daga Allah, ba wanda zai yi haka.

“Ba abin da za mu ce da Dauda Kahutu Rarara sai dai mu yi masa fata na alkairi. Allah ya saka masa da alkairi. Allah ya daɗo wasu mutane a wannan masana’antar tamu ta Kannywood irin su Dauda Kahutu Rarara.

“Kuma wallahi ni da gaske na ke yi, ya tallafa min kuma ina buƙatar tallafin. Na gode masa. Allah ya biya shi.”

Shi ma a nasa ɓangaren, mawaƙi Bello Ibrahim (Billy O) ya tabbatar wa da mujallar Fim cewa, ”Na karɓi dubu hamsin kamar yadda aka umarta, wanda daga garin Fatakwal aka yi min waya aka ce Rarara ya bada kuɗi a ba wa jarumai kuma har da suna na a ciki. Kuma alhamdu lillahi furodusa Maishadda ya same ni ya ban N50,000 kuma na karɓa a hannu na.”

Billy O ya kuma yi jan hanakali kamar haka: “Kamar yadda wannan mawaƙi ya bada wannan tallafin, kamata ya yi a ce mu ma mu na taruwa mu na taimaka wa mutane, musamman ‘yan Arewa, to da za a samu ci gaba sosai.

“Kuma hakan da ya yi ba ni kaɗai ya taimaka wa ba, mu na da yawa a Kannywood. Ka ga zai samu lada. Gaskiya na ji daɗi.

“Kuma shawara shi ne ina ma dukkan mu shawara mu dinga yin haka.”

Auwalu Zomuleƙa, wanda shi ma ya amfana da kuɗin tallafin, ya bayyana tallafin a matsayin wani abu da aka saba yi masa, ba wai shi ne karo na farko ba.

“Na ji daɗi sosai. Kuma da man ai shi ya saba yin irin wannan abubuwan, domin akwai wani lokaci da na yi jiyya kuma ya na ɗaya daga cikin waɗanda su ka ba ni babbar gudunmawa. Na ji daɗi sosai.

 

“Allah ya saka masa da alkairi, kamar yadda ya ke taimaka wa al’umma, shi ma Allah ya taimake shi, sannan Allah ya yi ba shi ninkin abin da ya yi mana.”

Su ma matan da su ka amfana da tallafin sun bayyana farin cikin su dangane da hakan tare da yin jinjina ga mawaƙin.

Ladidi Abdullahi (Tubeless) ta bayyana wa mujallar Fim cewa, Lokacin da aka kira ni ake sanar da ni, ina zaune ne a cikin gida tare da ‘yan’uwan mu aka kira ni a waya aka sanar da ni, aka ce, ‘Kin ga sunan ki a cikin waɗanda za a ba wa dubu hamsin.’ Na ce, ‘Na me?’ Aka ce na tallafin Rarara na azumi. Waallahi sai da na yi ihu don jin daɗi duk kuma da cewa wannan ba shi ne tallafi na farko da ya ba ni ba!

“Sannan waɗanda mu ke tare da su a lokacin da aka gaya min su ka ji sai da na yi musu alkairi su ma, kuma su ka gode masa su ka ji daɗi. To ka ga wannan ai abin alfahari ne.”

Kuma maganar gaskiya, da na zata Rarara ya manta da ni, don na ma cire rai, amma da aka ba ni wannan tallafi kuma aka ba ni na baya shi ma dubu hamsin, na ce gaskiya wannan mutumin ya na tare da mu, bai manta da mu ba ashe.

“Na gode. Ubangiji Allah ya masa sakayya da gidan Aljanna.”

Ita ma Asma’u Sani ta bayyana farin cikin ta, inda ta yi wa Rarara addu’o’in samun buɗi a rayuwar sa.

Sai dai kuma wasu jarumai da su ka amfana da tallafin sun noƙe sun ƙi yin magana lokacin da wakilin mu ya tuntuɓe su don jin ta bakin su game da wannan abin alheri da Rarara ya yi.

Mujallar Fim.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *