fbpx
Wednesday, October 20
Shadow

‘Yan Iran 82 suka mutu a hatsarin jirgin sama

Jirgin saman Ukraine da yayi hatsari a Iran na dauke da ‘yan kasar Iran 82.
Ministan harkokin wajen Iran Vadym Prystaiko ne ya tabbatar da hakan inda ya bayyana cewa akwai ‘yan Birtaniya uku da hatsarin ya rutsa da su wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutum sama da 170.

Sauran ‘yan kasashen da hatsarin ya rutsa da su kamar yadda ministan ya shaida sun hada da:
‘Yan Canada 63
‘Yan Ukraine 11, ciki har da ma’aikatan jirgin
‘Yan kasar Sweden 10
‘Yan Afghanistan hudu
‘Yan kasar Jamus uku
Ofishin jakadancin Ukraine da ke Tehran ya bayyana cewa matsalar inji ce ta yi sanadiyar hatsarin jirgin ba wai harin ta’addanci ba.
BBChausa.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *