fbpx
Tuesday, June 15
Shadow

Yan kasuwar Albasa sun yi barazanar dakatar da kai Albasa zuwa kudancin Najeriya daga ranar Litinin 7 ga Yuni

Kungiyar Yan Kasuwar Albasa ta Najeriya (OPMAN) ta ce za ta katse kai albasa ga daukacin kudancin Najeriya daga ranar Litinin, 7 ga watan Yuni, idan Gwamnatin Tarayya ta kasa amsa bukatun kungiyar.

Da yake jawabi ga ‘yan jarida bayan taron kungiyar a Sakkwato a karshen mako, Shugaban OPMAN, Aliyu Isa, ya lura cewa mambobin kungiyar sun yi asarar albasa da kadarori na kimanin Naira biliyan 4 da rabi a hare-hare daban-daban a kudu.

Isa ya ce a lokacin rikicin Aba a jihar Abia, kungiyar ta rasa mambobinta uku, yayin da kimanin tirela 30, motocin amfani 9, shagunan 50 da buhunan albasa 10,000, da sauran abubuwa masu muhimmanci na mambobinsu.

Hakama a garin Shasa na jihar Oyo, ya ce an yi asarar rayuka 27, tirela biyar, buhun albasa 5,600, motocin amfani 12 da sauran kayayyaki masu daraja.

Isah ya ce daya daga cikin bukatun na OPMAN shi ne cewa membobin kungiyar da suka yi asara sakamakon rikicin kabilanci da addini a Kudancin dole ne a biya su yadda ya kamata

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *