fbpx
Monday, November 29
Shadow

‘Yan Kudu zasu tallafawa Matarnan, Inyamura da gwamnan Borno ya girmama kan zuwa Aiki da wuri da Naira Miliyan 1

Bayan da gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagaba Umara Zulum ya taimaki matarnan Inyamura, Obiageli Mazi malamar Makaranta a Borno da ya samu ta zo wajan aiki da wuri inda ya bata kyautar Naira Dubu 100 sannan kuma ya kara mata mukami zuwa mataimakiyar shugaban makarantar, wasu daga kudancin kasarnan naso su su taimaka mata da kudi.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Wani shahararrrn me amfani da shafin Twitter kuma malamin makaranta, Dr. Dipo Awojide ya fara wannan kira inda yace yayi alkawaein zai bata Naira Dubu 75 sannan yayi kiran da a tara mata a kalla Naira Miliyan 1.

Tuni dai Hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad ya jinjinawa wannan yunkuri kumabya sha alwashin cewa zai hada su da mutumin da zai gano musu matar.

Dipo ya bayyana cewa sun samu daya daga cikin hadiman gwamnan Borno da yace zai taimaka musu akan wannan lamari.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *