fbpx
Wednesday, May 12
Shadow

Yan Nageriya keda kashi 60 na laifukan da ake aikata wa a kasar Ghana – Shugaban yan Nageriya Mazauna Ghana

Shugaban al’ummar Najeriya a Kasoa, Nana Kessington Oledo, ya bayyana cewa ‘yan uwansa‘ yan Nijeriya suna da alhakin shida daga cikin laifuka goma da aka aikata a yankin.

Lamarin, in ji shi, ya kasance babban abin damuwa ga kwamandan ‘yan sanda na yankin, wanda a koyaushe yake yi masa korafi don ya taimaka masa wajen dakile matsalar.

An bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa a gidan rediyon Accra 100.5FM, wacce ta maida hankali kan yanayin tsaro a yankin na Ghana.

A cikin gudummawar da ya bayar, shugaban na Najeriya ya ce ya ga abin takaici yadda hukumomin karfafa doka, Hukumar ‘yan sanda da Hukumar Shige da Fice ta Ghana, yadda suka ba da dama wasu yan Nageriya na ba su cin hanci da rashawa.

Yace wannan abun kunya ace kashi 6% daga cikin 10% na kararrakin laifuka da ake Kaiwa yan sandan kasar, yan Nageriya ne keda kaso 6%.

Yace dole ne suyi aiki tukura domin yakin da wadannan masu aikata laifukan saboda kada su gurbata sauran al’ummomin kasar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *