fbpx
Thursday, December 2
Shadow

‘Yan Najeriya basu faye amfani da Kwaroron robaba wajan Jima’i ba

Wani sabon bincike ya nuna cewa kashi 34 cikin 100 ne kadai na ‘yan Najeriya suke amfani da kwaroron roba yayin jima’i, kuma cikin wannan yawan kashi 28 cikin 100 ne kawai ke amfani da shi ko yaushe.

Kungiyoyin da suka hada kai wajen yin binciken sun hada da cibiyar NOI Polls mai yin bincike kan wasu al’amura a Afirka Ta Yamma da Hukumar Takaita Yaduwar Cutar AIDS NACA da kuma Gidauniyar AIDS HealthCare Foundation (AHF).
Shugaban NOI polls Dr Chike Nwangwu, Dr Chike Nwangwu, ya shaida wa BBC cewa duk da cewa kashi 83 cikin 100 na ‘yan Najeriya sun yi amannar cewa mutanen kirki ne kawai ke amfani da kwaroron roba, kuma kashi 34 ne kawai suka yarda suke amfani da shi.
“Kuma ko cikin kashi 34 din ma kashi 28 ne kawai ke amfani da shi ko yaushe.”
An fitar da rahoton ne don bikin Ranar Kwaroron Roba ta Duniya (ICD), da ake yi duk 13 ga watan Fabrairu, kwana guda kafin ranar Valentine, don wayar da kai kan masu son yin jima’i da kariya, ake kuma karfafa wa mutane su yi amfani da kwaroron roba.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *