fbpx
Friday, April 23
Shadow

Yan sanda 10 suka ji rauni a hatsarin ayarin motocin Gwamnan Bauchi

Akalla ‘yan sanda 10 da ke cikin ayarin motocin Gwamnan Bala na jihar Bauchi sun samu raunuka a wani hatsari a ranar Litinin.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa hatsarin ya faru ne yayin da gwamnan ke duba aikin hanya mai tsawon kilomita 60 a karamar hukumar Tafawa Balewa.
An tsara hanyar ne domin hada mutanen karamar hukumar Tafawa Balewa zuwa Yelwan Duguri da kewayen karamar hukumar Alkaleri ta jihar.
Wakilin NAN wanda ya ga hatsarin, ya ce Toyota Hilux din da ke dauke da jami’an ‘yan sandar sun kauce daga kan hanya da misalin karfe 1:30 na rana kuma suka wuntsila sau biyu bayan sun motar ta kucci masu a sakamakon kura ta sa gani yayi karanci.
Sai dai, ba a rasa rai ba amma dukkan jami’an ‘yan sanda da hatsarin ya rutsa da su an garzaya da su babban asibitin Bununu da ke karamar hukumar Tafawa Balewa don yi musu magani.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *