fbpx
Thursday, August 5
Shadow

Yan sanda jihar Imo sun kama mutane shida masu garkuwa da mutane, tare da ceto mutum daya

Michael Abattam, Jami’in Hulda da Jama’a na ’Yan sanda na Jihar, a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai, ya ce an kama wadanda ake zargin masu satar mutanen a gefen ruwan Tebegbe da ke jihar Delta.

Sanarwar ta ce, rundunar ‘yan sanda da ke cikin dabara sun yi nasarar kutsa kai cikin maboyar masu garkuwar inda aka kame su duka. Kuma aka hada wadda suka sace da danginta.

“A yayin bincike, mutane ukun da ake zargin sun ba da kansu ne ta hanyar amfani da bayanai wanda hakan ya ba rundunar damar kame wasu.

“Yayin da tawagar dabarun ke rakiyar wadanda ake zargin a wajen maboyarsu, daya daga cikinsu, Terry Mez, yayi kokarin guduwa kuma aka harbe shi a kafa don hana shi tserewa daga doka.

A yayin haka, sunayen wadanda ake zargin sun hada da Willine Ebefal daga Ogbokuno a jihar Delta, Terry Mes mai shekaru 31 daga Aguleri a jihar Anambra, Obasanjo Kimakia mai shekaru 20 daga karamar hukumar Burutu a jihar Delta, Augustine Irishaye mai shekaru 21, da Jennifer Awolowo mace, mai shekaru 16. .

Sanarwar ta ci gaba da cewa nan ba da dadewa ba za a gurfanar da wadanda ake zargin zuwa kotu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *